Japan ta yi nadama ga kasashen da ta ba wahala a yakin duniya na biyu
Firaministan Japan Shinzo Abe ya ce kasarsa ta yi nadama ga ta’asar da ta aikatawa kasashen Asiya, shugaban ya fadi haka ne a jawabinsa na cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu da aka samu galaba akan kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jawabin Shugaban dai dama ce ga Japan na farfado da dangantakarta da China da kuma Korea ta Kudu, kasashen da suka sha wahala a hannunta a lokacin yakin duniya na biyu.
Firaministan ya fadi kalamai, na neman gafara da ta’asar da Japan ta aikata a cikin jawabinsa.
Dakarun Japan dai sun mika wuya a lokacin da aka samu galaba akan su a 1945.
China tace sama da mutanen kasarta Miliyan 20 Japan ta kashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu