Isa ga babban shafi
Isra'ila

An kulla yarjejeniyar sabuwar Gwamnatin dake bawa bangaren yahudawa muhimmaci

Bayan Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kulla yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnati, shugaban kuma ya ba bangaren masu tsananin kishin yahudawa muhimmaci a wata sabuwar yarjejeniya da suka kulla.Wannan matakin dai ya fusata Falasdinawa wadanda Isra’ila ke ci gaba da mamaye yankunansu a gabacin Birnin Kudus.

Firiya Minista Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firiya Minista Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya yi nasarar cim ma yarjejeniya tsakanin shi da bangarorin siyasar Isra’ila da yammacin Laraba bayan shafe tsawon makwanni 6 firimiyan na tattauna batun kafa sabuwar gwamnati.
 

An cim ma yarjejeniyar ne dab da wa’adin Netanyahu ya cika.
 

A karkashin yarjejeniyar, Netanyahu ya ba bangaren ‘yan kishin yahudawa muhimmaci wadanda ke nuna goyon bayansu ga mamayar da Isra’ila ke yi wa yankunan Falasdinawa.
 

Wannan matakin kuma ana ganin zai kara dakushe dangantar da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa

Masana dai na ganin babu wani sauyi da za’a samu a nan gaba game da muradun Isra’ila akan Falasdinawa.

A yau Alhamis Isra’ila ta sanya hannu kan kwantaragin gina sabbin gidaje 900 a gabacin birnin Kudus jim kadan bayan Netanyahu ya sanar da kafa sabuwar gwamnati.

Gwamnatin Barack Obama na Amurka dai na ci gaba da bayyana damuwarta akan yadda Isra’ila ke mamayar yankunan Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.