Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Gwamnatin Israela, ta amince da gina Gidaje 381 a yankunan Palesdinawa

Gwamnatin Firaiministan Israela Benyamin Netenyahu ta amince da gina wasu karin sabbin Gidaje 381 a wata unguwa da ke wajen birnin Jerusalem

Colônia ortodoxas de Betar Ilit, criado em 1985, que cresceu 17% a mais que em 2002, e calcula-se que abrigue cerca de 20 mil pessoas.
Colônia ortodoxas de Betar Ilit, criado em 1985, que cresceu 17% a mais que em 2002, e calcula-se que abrigue cerca de 20 mil pessoas. REUTERS/Baz Ratner
Talla

A daidai lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai ke yi wa hukumomin Isra’ila matsin lamba domin kawo karshen gina sabbin gidaje a yankunan Palasdinawa da suka mamaye, bayanai na nuni da cewa gwamnatin Benyamin Netenyahu ta amince da gina wasu sabbin gidaje 381 a wata unguwa da ke wajen birnin Jerusalem.

Wannan dai shi ne karo na uku da Gwamnatin Tel Aviv ke bayar da izinin gina gidajen daga lokacin da ta soma sakin fursunoni da ke tsare a gidajen kasonta, kamar dai yadda Giyat Zeev mai magana da Yawun wata Kungiya ta Yahudawa da ke adawa da wannan shiri ya bayyana.

Wannan matakin dai ya zo ne akalla Makwanni 3 bayan da Israela ta saki wasu Fursunoni ‘yan kasar Palesdinu, bisa yarjejeniyar samar da zaman lafiya tsakanin Israela da Palesdinu da kasar Amurka ke jagoranta.

Wannan kuma shi ne karo na 3 da Gwamnatin Israela ke amincewa da kara giggina Gidaje a yankunan Paledinu abinda ke nuna cewar Firaiministan israela baya da niyyar samar da zaman lafiya tsakanin kassahen guda Biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.