Isa ga babban shafi
Afghanistan-ISIS

ISIS ta dauki alhakin mummunan harin da aka kai Afghanistan

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin wani mummunan harin kunar bakin waken da yayi sanadiyyar rasa ran a kalla mutane 33, wasu fiye da 100 suka sami raunuka a gabashin kasar Afghanistan. Shugaban kasar ta Afghanistan Ashraf Gahni ne ya bayya haka, kuma dama a baya gwamnatin kasar tayi ta bayyana yuwuwar mayakan na IS su iya shiga kasar.Sai dai har yanzu kungiyar ta ISIS bata bayyana cewa ta samu kaiwa kasar ta Afghanistan ba, amma kuma akwai alamu ‘yan kungiyar Taliba da dama sun canza sheka zuwa ISIS din.Da alama wannan ne karon farko da mayakan na IS suka kai wani gagarumin harin a kasar ta Afghanistan. 

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani
Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani REUTERS/Jonathan Ernst
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.