Isa ga babban shafi
Afghanistan

Za a kafa gwamnatin hada-ka a kasar Afghanistan

‘Yan takara biyu a zaben shugabancin kasar Afghanistan Ashraf Ghani da Abdullah Abudllah a yau lahadi sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin-kan kasa ta hanyar raba mukamai a tsakanin bangarorin biyu.  

Abdullah Abdullah da Ashraf Ghani
Abdullah Abdullah da Ashraf Ghani REUTERS/Jim Bourg
Talla

Karkashin wannan yarjejeniya dai Ghani wanda tsohon ma’aikacin bankin duniya ne, zai ksance shugaban kasa yayin da Abdullah tsohon ministan harkokin wajen kasar zai nada wanda yake so a matsayin firaminista.

A cikin watan Yunin da ya gabata ne aka gudanar da zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar wanda sakamakonsa ya bai wa Ashraf Ghani nasara, to sai dai abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah ya ki amincewa da sakamakon bisa zargin cewa an tafka magudi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin kawance na NATO karkashin jagorancin Amurka ke shirin ficewa daga kasar a karshen wannan shekara ta 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.