Isa ga babban shafi
Iraqi

An yi wa Mayakan IS taron dangi a Iraqi

Sojin kasar Iraqi tare da daruruwan Mayakan sa-kai mabiya Shi’a da na Kurdawa sun kaddamar da sabon farmaki na hadin kai a yau Assabar domin fatattakar mayakan IS da suka mamaye arewacin kasar. Dakarun na Iraqi sun doshi yankin Amerli domin kwato yankin da ya fada ikon Mayakan IS da suka kaddamar da gwagwarmayar shinfida sabuwar daular Musulunci sama da wata biyu.

Sojojin Kurdawa rike da tuta bayan sun fafata da mayakan IS a Jalawla
Sojojin Kurdawa rike da tuta bayan sun fafata da mayakan IS a Jalawla Reuters
Talla

Rahotanni sun ce mazauna yankunan da Mayakan na IS ke iko suna cikin hali na karancin abinci da matsalar ruwan sha, sannan kuma rayuwarsu na cike da hatsari saboda akidar Shi’a da suke bi.

Babban hafsan Sojin Iraqi Janar Abdul’amir al-Zaidi yace sun kaddamar da farmakin tare da yi wa Mayakan ruwan wuta da jiragen yaki domin kubutar da al’ummar yankin Amerli daga hannun Mayakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.