Isa ga babban shafi
Myanmar

Mabiya Budda sun yi wa Kamfanin sadarwa na Qatar tawaye

Limamman addinin Budda masu tsatsauran ra’ayi a kasar Burma sun yi kiran kauracewa kamfanin sadarwar wayar salula na kasar Qatar Ooredoo a matsayinsa na mallakin kasar Musulmi, duk kuwa da alkawarin da kamfanin ya yi na kara fadada samar da wayoyin sadarwa a cikin farashi mai sauki a kasar.

Mabiya Addinin budda a kasar Thailand
Mabiya Addinin budda a kasar Thailand Reuters
Talla

Kamfanin wayar salula na Ooredoo tare da na kasar Norvégien Telenor ne, suka yi nasarar samun iznin kafuwa a kasar Burma, wanda ya sa suka zama na farko da suka fara kutsa kai a kasar da ke da karancin wayoyin sadarwa a duniya.

Kamfanonin biyu sun fara sayar da layukan wayoyinsu ne a cikin wannan shekara a kasar Burma, kasar da ta kasance mutun daya cikin 10 ne kawai suka mallaki wayar salula saboda tsadar sadarwa.

Kasar Burma dai na fuskantar tashe tashen hankula daga kungiyoyin ‘yan Budda musamman limammansu masu tsatsauran ra’ayi tare da kuma nuna kin jinin musulmi ‘yan tsirari a kasar. hakan ya sa suka yi kiran da a kauracewa dukkanin shagunanan sayar da layukan salula na musulmi tare da neman ganin gwamnati ta samar da doka da zata takaita aure tsakanin mabiya addinan kasar.

har ila yau limaman addinin na Budda masu tsatsauran ra’ayi, sun nuna bacin ransu da lasisin izinin kafuwa da gwamnatin kasar ta bai wa kamfanin Ooredoo mallakar gwamnatin Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.