Isa ga babban shafi
Myanmar

HRW ta yaba wa Myanmar game da sakin Fursunonin siyasa

Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Human Rights Watch ta yaba wa gwamnatin kasar Myanmar a game da shirin yi wa dukkanin fursunonin siyasa na kasar Afuwa. Sai dai kuma akwai sauran manyan ‘yan siyasa da ke fuskantar tuhuma tun lokacin da aka kawo karshen adawa da mulkin Soji shekaru uku da suka gabata.

Yan Naing Tun, tare da dinbim mutanen kasar Myanmar da ke murnar shirin sako fursononin siyasa a Myanmar
Yan Naing Tun, tare da dinbim mutanen kasar Myanmar da ke murnar shirin sako fursononin siyasa a Myanmar REUTERS/Soe Zeya Tun
Talla

David Mathieson, jami’in kungiyar ta Human Rights yace suna iya cewa wannan wani muhimmin ci gaba ne daga bangaren gwamnatin Myanmar, ta la’akari da yadda aka tsara yin afuwar a cikin kwanaki 5 masu zuwa inda za’a ‘yantar da dukkanin fursunonin kasar.

Masu fafutika dai suna fatar gwamnatin kasar zata saki daukacin daruruwan mutane da ke fuskantar caje-caje daban daban.

Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch ta bayyana fatar gwamnatin Myanmar za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye ga dokokin kasar domin kawo karshen danniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.