Isa ga babban shafi
Pakistan-Amurka

Kerry ya soke ganawa da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas

Shirin samar da zaman lafiya tsakanin Palasdinawa da Isra’ila na baranar rugujewa bayan Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yanke shawarar soke kai ziyarar ai yankin biyo bayan shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya ce zai tunkari Majalisar Dinkin Duniya dangane da yadda Isra’ila ke ci gaba da gina gidaje a yankunan da ta mamaye.

John Kerry da Mahmud Abbas
John Kerry da Mahmud Abbas REUTERS/Evan Vucci/Pool
Talla

Yau laraba ne dai ya kamata Kerry ya sake komawa a Ramallah domin ganawa da Abbas, to amma sai ya sanar da soke kai wannan ziyara jim kadan bayan da hukumomin Palasdinu suka sanya hannu kan wasu yarjeniyoyin Majalisar Dinkin Duniya cikinsu kuwa har da na kare hakkokin bil’adama.
Isra’ila da Amurka dai na kallo hakan a matsayin wani mataki da ya keta haddi, ta la’akari da cewa har yanzu Palasdinu na da kwarya-kwaryan ‘yancin cin gashin kai ne amma ba cikakkiyar kasar da za ta iya gudanar da irin wannan hulda na MDD ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.