Isa ga babban shafi
Korea

Korea ta Arewa da Kudu sun hau teburin sulhu

A karon farko bayan kwashe shekaru 9, Kasashen Korea ta Arewa da Korea ta Kudu sun gudanar da zaman tattaunawar sulhu a tsakaninsu a wani mataki na inganta hulda tare da kawo ƙarshen barazanar yaƙi da suke yi wa juna.

Wakilin Korea ta Arewa Park Yong Il yana taɓewa da wakilin Korea ta Kudu Lee Duk-haeng
Wakilin Korea ta Arewa Park Yong Il yana taɓewa da wakilin Korea ta Kudu Lee Duk-haeng REUTERS/Unification Ministry/Yonhap
Talla

Akwai batun tsagaita wuta da bangarorin biyu ake sa ran zasu cim ma a ƙauyen Panmunjom da suke hamayya da juna tare da tattauna ranakun da Ƴan uwa zasu gana da danginsu da suka rabu da su tun a lokacin yaƙin Korea da ya raba ƙasashen gida biyu.

Ɓangaorirn biyu sun amince Ƴan uwa su gana a tsakanin ranakun 20 zuwa 25 na watan Fabrairu.

Cikin zaman tattaunawar ana sa ran ƙasar Korea ta Arewa zata nemi Korea ta Kudu ta dakatar da atisayen Soji da zata gudarar tare da Amurka a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Da misalin ƙarfe 10 na safe agogon Korea ne wakilan ƙasashen biyu suka soma tattaunawar wanda masana suke ganin wani babi ne da zai samar da zaman lafiya a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.