Isa ga babban shafi
Bangladesh

‘Yan sandan Bangladesh sun budewa masu zanga-zanga wuta

‘Yan sandan kasar Bangladesh sun budewa masu zanga-zanga wuta wadanda ke adawa da hukuncin kisa da aka zartar wa Abdulkader Molla shugaban Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi. Rahotanni sun ce mutane 5 sun mutu, wasu da dama kuma suka samu rauni.

'Yan sandan Bangladesh suna arangama da magoya bayan Jam'iyyar  Jamaat-e-Islami da ke zanga0zangar la'antar hukuncin kisa da aka zartar wa shugabansu Abdulkader Mullah
'Yan sandan Bangladesh suna arangama da magoya bayan Jam'iyyar Jamaat-e-Islami da ke zanga0zangar la'antar hukuncin kisa da aka zartar wa shugabansu Abdulkader Mullah REUTERS/Andrew Biraj
Talla

‘Yan sandan sun ce rikicin ya barke ne a yankunan kudu masu gabashin Satkhira bayan zartarwa Molla hukuncin kisa a makon jiya.

‘Yan sanda sun yi zargin cewa akwai dunkulen bama bamai da ‘Yan rajin kare muradun Jam’iyyar Jamaat-e-Islami da suke ke harba wa a ofishinsu da shingayen bincike.

Babban Jami’in ‘Yan sanda a kasar Kazi Moniruzzaman ya tabbatarwa Kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa sun budewa masu zanga-zangar wuta domin kare kansu a yankin Satkhira, al’amarin da ya yi sanadin mutuwar masu zanga-zangar guda biyar.

Zuwa yanzu akalla mutane 30 ne suka mutu tun lokacin da aka zartar wa Mulla hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar Alahmis.

Abdulkader Mulla shi ne mutum na farko da aka zartar wa hukuncin kisa daga cikin shugabannin Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi da ake tuhuma da aikata laifukan yaki a lokacin kwato ‘yancin kai daga Pakistan a 1971.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.