Bangladesh
An sami barkewar tashin hankali a kasar Bangladesh
An samu barkewar sabon tashin hankali a kasar Bangladesh yau Jumu’a, bayan da aka yankewa wani shaihin Malami hukuncin kisa bisa zarginsa da aikata laifin ta’addanci.Masu kishin Islama da dama ne suka fantsama akan Tituna suna nuna rashin jin dadin su akan aiwatar da hukuncin kisan da aka yiwa wanan Malamin.Abdul-Qader Molla, shi ne na farko da aka rataye saboda samun shi da hannu a zub da Jinin da aka yi a shekarar 1971, lokacin fadan samun ‘yancin kasar daga kasar Pakistan.
Wallafawa ranar: