Isa ga babban shafi

Al'ummar Senegal sun fara kada kuri'ar zaben shugabansu na biyar

Sama da mutane milyan 7 da dubu 300 ne suka cancanci kada kuri’a a zaben shugabancin kasa da ake gudanarwa wannan lahadi a Senegal, zaben da ke zuwa bayan share kusan shekaru uku ana fama da rikicin siyasa a kasar.Mutane 17 ne ke takarar a zaben na yau lahadi.

Shugaban kasar Senegal  Macky SALL ya na kada kuri'a
Shugaban kasar Senegal Macky SALL ya na kada kuri'a © senegali jamanaɲɛmɔgɔyaso
Talla

Mutane 17 ne ke takarar a zaben na yau, da suka hada da Amadou Ba dan takarar jam’iyyar mai mulki da ke samun goyon bayan shugaba mai barin gado Macky Sall, sai Bassirou Diomaye Faye da ke samun goyon bayan jagoran ‘yan adawa Ousman Sonko, yayin da a hannu daya akwai tsohon magajin garin Dakar Khalifa Sall.

Wasu daga cikin 'yan kasar Senegal a rufar zabe
Wasu daga cikin 'yan kasar Senegal a rufar zabe © Juliette Dubois/RFI

Jim kadan bayan ya kada kuri’arsa a garin Fatick da ke tsakiyar kasar, shugaba Macky Sall ya gargadi ‘yan takara da su yi taka-tsantsan domin kauce wa shelanta yin nasara bayan kammala zabe, yana mai cewa sanar da sakamako alhaki ne da ya rataya a wuyan hukumar zabe mai zaman kanta.

Jagoran ‘yan adawa Ousman Sonko, a zantawarsa da manema labarai bayan ya kada kuri’a a yankin Zinguinchor da ke kudancin kasar, ya yi hasashen cewa dan takararsa Bassirou Diomey Faye ne zai yi lashe wannan zabe.

Masu zabe a yankin Ndiaganiao dake  Mbour,a Sénégal.
Masu zabe a yankin Ndiaganiao dake Mbour,a Sénégal. REUTERS - Zohra Bensemra

Akwai dai tawagogin ‘yan kallo daga sassa daban daban, da suka hada da na Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma wato Ecowas/Cedeao, da Tarayyar Turai da kuma kungiyoyin fararen hula na cikin kasar da ke sa ido dangane da yadda zaben ke gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.