Isa ga babban shafi

Kotun Senegal ta amince da 24 ga watan Maris a matsayin ranar babban zabe

Kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar Senegal ta amince da 24 ga watan Maris a matsayin ranar da za a kada kuri’a a zaben shugaban kasar, kamar yadda shugaban kasar mai barin gado Macky Sall, ya bukaci a yi.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall. 25/10/23
Shugaban kasar Senegal Macky Sall. 25/10/23 REUTERS - JOHANNA GERON
Talla

A cewar kotun ta yi nazari sosai kafin ayyana 31 ga watan Maris a matsayin ranar kada kuri’a, amma sakamakon wasu sauye-sauye suka sanya dole aka rage ranar zuwa 24 ga watan.

Ana sa ran wannan mataki zai yayyafa ruwa kan rikicin da ake fama da shi a kasar sakamakon dage ranar zaben da Sall ya yi.

Shugaban da ya ke kan Mulki tun shekarar 2012 ya bayyana cewa ya dage ranar zaben ne, sakamakon zargin rashin cancantar wadanda suka tsaya takarar da kuma gudun kar hakan ya janyo tashin hankali a Senegal kamar yadda aka samu a shekarar 2021 da 2023.

Dagewar dai ta janyo cece-kuce a ciki da wajen kasar tare da zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.