Isa ga babban shafi

Macky Sall ya jaddada aniyar sauka daga mulki a ranar 2 ga watan Aprilu

Shugaba Macky Sall na Senegal ya bayyana cewa wa’adin mulkinsa zai kare a ranar 2 ga watan Aprilu kamar yadda doka ta tanada, kuma zai sauka daga mukami bisa sharadin samar da magajinsa, sai dai shugaban ya ce ya bar kofa a bude game da tsayar da ranar gudanar da babban zaben kasar.

Shugaba Macky Sall na Senegal.
Shugaba Macky Sall na Senegal. REUTERS - AMR ALFIKY
Talla

Macky Sall dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba wajen ganin ya tsayar da ranar gudanar da babban zaben kasar bayan dagewa daga ranar 25 ga watan nan kamar yadda aka tsara.

Tun farko Sall ya mayar da zaben zuwa watan Disamba amma kotun kundin tsarin mulkin kasar ta yi watsi da kudirin nasa bayan fuskantar tarzomar da ta kai ga asarar rayuka baya ga kulle tarin magoya bayan bangaren adawa.

A jawabin da ya gabatar daren jiya Alhamis wanda aka tsammaci ya sanar da ranar gudanar da zaben na Senegal, Macky Sall ya ce ko shakka babu mulkinsa zai kawo karshe a ranar 2 ga watan Aprilu kamar yadda ya karbi rantsuwar kama aiki a makamanciyar ranar cikin shekarar 2019.

Sai dai a cewar shugaban dole ne a samar da magaji da zai ci gaba da jan ragamar kasar bayan doguwar tattaunawar fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki.

A cewar Sall sai a nan gaba ne za a kammala tattaunawa kan takamaiman lokacin gudanar da zaben kasar, kalaman da ke kawo karshen jita-jitar cewa shugaban na son ci gaba da zama a madafun iko.

A Litinin mai zuwa ne bangarorin siyasar kasar za su shiga tattaunawa da juna  wanda zai kai ga bayar da damar jin ra’ayoyin al’ummar kasa.

A wani yanayi da ake kallo da yunkurin sassauta rikicin siyasar da Senegal ta fada, Sall ya bayyana cewa ya na duba yiwuwar sakin madugun adawa Ousmane Sonko da Bassirou Diomaye Faye wadanda ke tsare a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.