Isa ga babban shafi

Tattalin arzikin Afrika na habbaka cikin sauri

Tattalin arzikin kasashen Afrika na ci gaba da habbaka cikin gaggawa duk kuwa da wasu tarin matsalolin da nahiyar ke fama da su da suka hada da tsadar rayuwa da sauyin yanayi da tashe-tashen hankula da karancin abinci har ma da basuka.

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina.
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina. © REUTERS/Amit Dave
Talla

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika Dr. Akinwumi Adesina ne ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da jakadu da wakilan bankin da aka saba gudanarwa duk shekara, yana mai cewa, hakan na nuna irin juriyar da nahiyaar ke da ita.

An yi hasashen cewa, Afrika za ta samu kaso 11 daga cikin 20 na kasashen duniya da ke tattalin arziki mai habbaka cikin sauri a cikin wannan shekara ta 2024” Inji Adesina.

Wani fashin baki kan hanyoyin bunkasar tattalin arziki a sassan Afrika ya nuna cewa, Najeriya ta samu habbakar ma’aunin tattalin arzikinta da kashi 3.46 a cikin rubu’in karshe na shekarar da ta gabata kamar yadda shugaban na Bankin Afrika ya yi karin haske.

Tattalin arzikin Ghana kuwa ya samu jan kafa da kashi 2 a rubu’i na uku na shekarar bara, matsalar da ke da nasaba da koma-bayan da ma’aikatun kasar suka samu.

Kenya ta samu habbakar tattalin arziki da kashi 5.9 a rubu’i na uku na shekarar 2023 sakamakon farfadowar bangaren noma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.