Kasar Zimbabwe na shirin karbar tallafin hatsi daga Rasha
Kasar Zimbabwe ta tabbatar da shirin karbar kason farko na hatsi da Russia ta tura mata a matsayin tallafin magance matsalar karancin abinci da kasar ke fuskanta a sakamakon mamayar Ukraine da ta yi.
Wallafawa ranar:
A shekarar da ta gabata ne dai shugaba Vladimir Puttin ya tura hatsi kyauta ga wasu kasashen Afirka guda 6 ciki har da Zimbabwe, yayin wani taro da ya gudana a Saint Petersburg na neman a sahalewa Ukraine safarar hatsi ta tekun bahar maliya.
Bayan Zimbabwe, Putin ya alkawarta tura hatsin ga kasashen Mali, Somalia, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Eritrea da kuma Burkina Faso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu