Kakakin majalisar Cuba na ziyara a Kenya kan makomar likitocin kasar da ke hannun Al-shabab
Kakakin Majalisar Cuba na ziyara a Kenya don tattaunawa game da makomar likitocin kasar 2 da mayakan Alshabaab suka yi garkuwa da su a wani yanki na Nairobi shekaru 5 da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar harkokin wajen Kenya da ke tabbatar da ziyarar Esteban Lazo na zuwa ne bayan Al-Shabaab ta fitar da wata sanarwa da ke ikirarin cewa likitocin na Cuba biyu sun mutu sun mutu a luguden wutar da Sojin Amurka suka yi a sansanin mayakan kungiyar da ke Somalia cikin makon jiya.
Tun a ranar 12 ga watan Aprilun 2019 ne mayakan Al-Shabaab suka yi garkuwa da likitocin na Cuba guda 2 kuma tun daga wancan lokaci ake tattaunawar kubutar da sub a tare da nasara ba.
Lazo "ya kai ziyara zuwa Kenya domin tattaunawa da manyan hukumomin kasar kan makomar likitocin kasarmu da aka yi garkuwa da su", in ji sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Cuba.
Sanarwar ta ce, ma’aikatar harkokin wajen na kan tattaunawa da gwamnatin Somaliya, tare da neman tallafin gwamnatin Amurka a diflomasiyyance.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu