Isa ga babban shafi

Ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinmu barazana ce babba - ECOWAS

Ministan harkokin wajen Saliyo Timothy Kabba, ya bayyana janyewar Mali, Burkina Faso da kuma Nijar daga cikin ECOWAS a matsayin babbar barazana ga tsaron daukacin kasashen da ke cikin kungiyar.

Babban dakin taron Kungiyar kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya.
Babban dakin taron Kungiyar kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya. © MICHELE SPATARI / AFP
Talla

Kabba wanda ke cikin tawagar ECOWAS din da ke tattauna wa da sojojin da suka yi juyin Mulki a Nijar, ya ce matakin ficewar kasashen uku daga cikinsu, ka iya hargista zaman lafiyar baki dayan yankin yammacin nahiyar Afirka.

00:54

Ministan harkokin wajen Saliyo Timothy Kabba da ke tawagar ECOWAS mai tattauna wa da sojojin NijarNijar

Tuni dai kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta ce a shirye take ta shiga tattaunawar lalaubo mafita tsakaninta da Burkina Faso, Mali da kuma Nijar, wadanda ta bayyana a matsayin masu matukar muhimmanci gareta.

Bayanai dai na nuni da cewar kowane lokaci daga wannan wallafa, Nijar ka iya bin sahun takwarorinta  biyu wajen mika wa ECOWAS takardar neman ficewa daga cikinta a hukumance bayan sanarwar da suka fitar a a ranar Lahadin da ta gabata.

A karkashin dokokin ECOWAS dai ana bukatar akalla shekara guda wajen cika wasu ka’aidoji ga duk kasar da ke son ficewa daga cikin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.