Isa ga babban shafi

ECOWAS ta sha alwashin ci gaba da laluben maslaha ga Burkina, Mali da Nijar

Kungiyar kasashen yammacin Afrika, ECOWAS ko CEDEAO ta mayar da martani a kan sanarwar ficewar Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar daga cikinta.

Shugabannin ECOWAS a taronsu a birnin Abujan Najeriya.
Shugabannin ECOWAS a taronsu a birnin Abujan Najeriya. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Ko da ya ke kungiyar ta ce har yanzu ba ta samu wata wasika da ke nuni da hakan daga kasashen uku a game da aniyarta ta janyewa daga cikinta ba, duk da haka har yanzu tana kan bakarta ta ganin cewa an lalubo masalaha hanyar tattaunawa a kasashen.

A wata  sanarwar da ECOWAS ta fitar, ta  jaddada aniyarta ta aiki sau da kafa da Burkina Faso, Mali, da Jamhuriyar Nijar don maido da aiki da kundin tsarin mulki a cikin su.

ECOWAS ta kuma jaddada mahimmancin Burkina Faso, Nijar da Mali a matsayinsu na mambobinta.

Har yanzu dai sojojin da suka kifar da gwamnatocin farar hula ne suke jan ragamar wadannan kasashe da ke fama da matsalar tsaro a yammacin nahiyar Afrika.

A wannan Lahadin ce kasashen  uku suka sanar da matakin da suka dauka na ficewa da ECOWAS ba  tare da bata lokaci ba.

A wata sanarwa, kasashen uku na yammacin nahiyar Afrika sun ce ECOWAS ko CEDEAO ta sauka daga kunshin muradan da wadanda suka kafa ta suka dora ta, saboda  haka suka zabi ficewa daga cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.