Isa ga babban shafi

Burkina, Mali, Nijar sun sanar da ficewa daga ECOWAS/CEDEAO nan take

Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashen Yammacin nahiyar Afirka, ECOWAS ba tare da bata lokaci ba.

Shugabannin kasashen ECOWAS yayin taronsu a Abuja.
Shugabannin kasashen ECOWAS yayin taronsu a Abuja. © KOLA SULAIMON / AFP
Talla

Wannan na kunshe ne a wata sanarwar hadin gwiwa da da kasashen uku suka fitar a wannan Lahadi, inda suka ce sun bar wannan kungiya ta ECOWAS ko CEDEAO.

Sanarwar da aka karanta a kafofin yada labaran kasashen uku ta ce jagororin kasashen sun dauki wannan mataki ne da cikakken goyon bayan al’ummarsu.

 

Dangantaka ta yi tsami tsakanin wadannan kasashe sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi a cikinsu, lamarin da ya  janyo takun-saka tsakaninsu da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, sakamakon takunkuman karayar tattalin arziki da kungiyar ta sanya  musu.

 

Kasa ta baya bayan na da ta shiga takun-saka da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ita ce Jamhuriyar Nijar, wadda sojoji suka kifar da gwamnatin Dimmokaradiyya a ranar 26 ga watan Yulin shekarar da ta gabata, kuma aka gaza fahimtar juna tsakaninta  da kungiyar ta kasashenn yammacin nahiyar Afrika.

Kwanan nan ne ECOWAS ta dage wata tattauwanwa da ta shirya yi da jagororin sojin Nijar, amma daga baya ta bada uzurin cewa jirgin da ta yi haya zai dauki tawagarta ne ya lalace a birnin Abuja na Najeriya, tana mai cewa za ta sanar da lokacin da za a yi wannan tattaunawa nan gaba kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.