Isa ga babban shafi

Fararen hula da dama ne aka kashe a yankin kan iyakar Nijer da Burkina Faso

Gwamnatin sojin Nijar ta tabbatar da mutuwar fararen hula da dama, wadanda dakarun kasar suka gano gawarwakinsu, bayan harin saman da suka kaddamar kan gungun ‘yan ta’adda a kusa da iyakar kasar da Burkina Faso.

Ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar Hama Adamou Souley, yayin ziyarar garin Tamou
Ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar Hama Adamou Souley, yayin ziyarar garin Tamou © niger
Talla

Cikin sanarwar da suka fitar a ranar Asabar, sojojin da ke mulkin Nijar, sun ce lamarin ya auku ne ranar Juma’ar da ta gabata, a lokacin da rundunar sojin kasar ta yi amfani da jirgin yaki maras matuki, wajen dakile harin da gungun ‘yan ta’adda haye kan babura kimanin 20 suka kai kan wani sansanin soji da ke yankin Tyawa a yammacin jihar Tillaberi.

Bayan ruwan wutar da aka yi wa ‘yan ta’addan ne, a yayin da kuma ake sake bibiyar yankin, sojoji suka gano fararen hular da lamarin ya rutsa da su, wadanda sojin basu bayyana adadinsu ba.

Sai dai wasu majiyoyi daga mazauna yankin na Tyawa sun ruwaito cewar, adadin fararen hular da suka rasa rayukansu ya haura mutane 50.

Gwamnatin Nijar din dai ta ce, tuni aka fara bai wa wadanda suka jikkata yayin kokarin dakile harin ta’addancin kulawa, bayan da aka kwashe su daga garin.

Kamar Mali da Burkina Faso, Nijar ma ta dade tana fama da hare-haren ‘yan ta’adda, musamman a yankunanta da ke yi iyaka da kasashen biyu da take makwaftaka da su, inda ko a karshen watan Disamba sai da fararen hula 11 suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.