Isa ga babban shafi

Daliban Najeriya dubu 15 za su shiga tsaka mai wuya bayan haramta digirin Benin

Kungiyar Daliban Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar ta sake nazarta matakin haramta digirin Jamhuriyyar Benin a cikin kasar lura da yadda hakan zai shafi akalla dalibai dubu 15 da yanzu haka ke tsaka da karatu a Coutonu.

Wasu daliban Najeriya.
Wasu daliban Najeriya. Premium Times Nigeria
Talla

Matakin haramta amfani da digirin ta Benin ya biyo rahoton yadda wani dan jarida ya yi basaja tare da kammala digirinsa cikin watanni 2 a kasar tare da dawowa Najeriyar don fara bautar kasa.

Dangane da wannan dambarwa ne gwamnatin Najeriyar ta haramta digirin daga makwabciyarta yayinda daga bisani ta fadada haramcin zuwa wasu kasashe da suka kunshi Uganda da Kenya da kuma Togo da Ghana baya ga Jamhuriyar Nijar.

Sai dai shugaban kungiyar daliban Najeriya da ke karatu a Benin Ugochukwu Favour yayin zantawarsa da gidan talabijin na Channels ya roki gwamnatin kasar kan ta sake nazartar matakin tare da tantance ingancin jami’o’in gabanin zartas da makamancin hukuncin.

A cewar shugaban na NAN akwai bukatar hukunta iya jami’ar da aka samu da tafka badakalar maimakon yin kudin goro ga ilahirin jami’o’in da ke Benin.

A cewarsa yanzu haka akwai daliban Najeriya fiye da dubu 15 da ke karatu a jami’o’I daban-daban da ke cikin kasar ta Benin, kuma daukar matakin kai tsaye zai wargaza rayuwarsu.

Sai dai ministan Ilimi na Najeriya, Tahir Mamman ya bayyana cewa baya ko tausayawa daliban da ke karatu a kasashen da aka haramta, maimakon haka ma kamata ya yi a tuhume su da aikata babban laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.