Isa ga babban shafi

Makomar ayyukan wanzar da zaman lafiya na Dakarun Majalisar Dimkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka na nazari kan makomar ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen Duniya.

Taron kungiyar kasashen Afrika
Taron kungiyar kasashen Afrika © CPHIA2023
Talla

Makomar ayyukan wanzar da zaman lafiya a Afirka na kara zama al’amarin tambaya yayin da kasar Mali ta bukaci ficewar dakarun Minusma a watan Yunin 2023, baya ga Mali Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ta bukaci janyewar wadanan dakaru kama daga watan Disamba. Ganin wadanan korafe-korafe Majalisar Dinkin Duniya ta soma nazari  domin fayyace hanyoyin tunkarar haka da kuma  barazanar 'yan ta'adda da masu dauke da makamai a nahiyar Afirka.

Yayin taro karo na bakwai  tsakanin Majalisar Dimkin Duniya da kungiyar kasashen Afrika, Wakilan kungiyoyin biyu sun kuma rattaba hannu kan wata yarjejeniyar mutunta hakkin dan Adam.

Ga shugabannin Tarayyar Afirka da na Majalisar Dinkin Duniya, ayyukan wanzar da zaman lafiya kamar yadda ake zato shekaru da dama da suka gabata ba su da alaka da mayar da martani ga karuwar tashe-tashen hankula a kasa.

 Lokaci ya yi da za a sauya tsarin, in ji Moussa Faki, shugaban hukumar Tarayyar Afirka.Moussa Faki ya na mai cewa “dole ne albarkatun Majalisar Dinkin Duniya su dauki nauyin wadannan ayyuka na Afirka. Wannan barazana ce ga zaman lafiya da tsaro, kuma wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya."

Antonio Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya tabbatarwa wakilan Afrika cewa: Kungiyar Tarayyar Afirka na da karfin aiwatar da wadannan ayyuka.

"Dokokin bin ka'idojin da Tarayyar Afirka ta kafa sun yi daidai da namu," in ji Antonio Guterres. Kuma yarjejeniyar da suka  cimma a yau game da kare hakkin bil adama, wani karin tabbaci ne na cewa za su iya amincewa da kungiyar Tarayyar Afirka wajen shirya ayyukan wanzar da zaman lafiya a Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.