Isa ga babban shafi
Rahoto

Faransa za ta taimaki Najeriya wajen yaki da sauyin yanayi a Afrika

Kasar Faransa ta kaddamar da wani shirin taimaka wa Najeriya da wasu kasashen Afrika domin tunkarar matsaloli masu nasaba da sauyin yanayi, da suka hada da ambaliyar ruwa da dai sauransu. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayin wata ziyara a Faransa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayin wata ziyara a Faransa via REUTERS - POOL
Talla

 

Ku latsa alamar sauti domin sauraren rahoton Muhammad Kabiru Yusuf daga Abuja.    

A cewar Jakadiyar kasar Faransa a Najeriya Emmauelle Blatmann, Kasar  Faransa a shirye take ta taimaka domin kawar da wadannan matsaloli. 

Hukumar kasar Faransa mai kuda ci gaban kasashen, tana aiki da hadin gwiwar Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Najeriya wajen yaki da dimamar yanayi da sauyinsa a Najeriya. Kasar Faransa na aiki ne ba dare ba rana tun lokacin da aka kulla yarjejeniyar nan a Kasar Faransa 

Kasashe Kamaru da Ghana da Rwanda na daga cikin kasashen da suka halarci taron da aka gudanar a ranar Litinin din nan a Najeriya, yayin da Shugaban Hukumar Hasashen Yanayin ta Ghana Eric Esuman, ke cewa suna bukatar samun hadin-kai a tsakaninsu don ceto rayukan 'yan Afrika

Na tabbata in mun hada kanmu za mu cike duk wani gurbi da ke tsakaninmu, mu kuma hada dabarunmu waje guda, na tabbata za mu ceto rayuka da dukiyoyin Al’umma. 

A nasa bangaren,  Farfesa Mansur  Bako Matazu, Shugaban Hukumar Hasashen Yanayin ta Najeriya ya bayyana cewa kasashen za su mayar da hankali wajen musayar bayanai a tsakaninsu, domin abin da ya shafi Ghana ya shafi kowannesu.

Shirin dai ya hada da kamfanoni 30 daga kasar Faransa da za su hada gwiwa da kasashen na Afrika domin cimma burin rage dumamar yanayi da canjinsa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.