Isa ga babban shafi

'Yan damfara sun saci kamannin shugaban Kungiyar AU

Wasu kwararrun ‘yan damfara sun yi amfani da sabuwar fasahar Kirkirarriyar Basira ta AI wajen bat da kama tare da gabatar da kansu a matsayin shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU, Moussa Faki, inda har suka tattaunawa da wasu shugabannin kasashen duniya ta hoton bidiyo.

Mossa Faki Mahamat, shugaban gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka
Mossa Faki Mahamat, shugaban gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka © Moussa Faki
Talla

Da ma dai bisa al’ada,   shugaban na Kungiyar Kasashen Afrika kan fara rubuta wasika ga shugabannin kasashen duniyar da yake son ganawa da su ta wayar tarho ko kuma hoton bidiyo.

Kuma wannan ita ce dadaddiyar al’adar da ya saba amfani da ita wajen tsayar da lokacin ganawa da shugabannin Kungiyar Afrika da sauran wakilan kasashen duniya har ma da manyan kungiyoyi.

Sai dai a wannan karon, kwararrun ‘yan damfarar sun yi amfani da muryar Mista Faki ta bogi, inda suka nemi gudanar da jerin ganawa da hukumomin biranen kasashen Turai da dama.

Kazalika, wadannan ‘yan damfarar sun kuma yi amfani da sakon imel na bogi, inda suka yi karyar gabatar da kansu a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan Kungiyar AU, suna neman tsayar da lokacin ganawa tsakanin Mista Faki da shugabannin kasashen waje.

A takaice dai, wadannan kwararrun ‘yan damfarar har sun gudanar da tattaunawar kafar bidiyo da wasu daga cikin shugabannin kasashen Turai, inda suka yi amfani da dabararsu wadda ta nuna hoton bogi na Mista Faki yana magana a bidiyon.

Kawo yanzu babu wani bayani kan musababbin abin da ya sa bata-garin suka aikata haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.