Isa ga babban shafi

Dokar haramtawa dalibai mata sanya nikabi a Masar ta janyo ce-ce-kuce.

Dokar haramta amfani da nikabi ko kuma kyallen rufe fuska ga mata a cikin makarantu ya haifar da cecekuce a  kasar Masar tun bayan da ma’aikatar harkokin Ilimin kasar ta sanar da matakin.

Iyayen dalibai a kasar nan ganin wannan hanya ce ta koyawa yaransu yaki da koyarwar addinin islama da ya umarci suturta jiki ga 'ya mace
Iyayen dalibai a kasar nan ganin wannan hanya ce ta koyawa yaransu yaki da koyarwar addinin islama da ya umarci suturta jiki ga 'ya mace AP - Ebrahim Noroozi
Talla

A safiyar ranar Litinin ne jaridu da kuma kafofin yada labaran kasar suka wayi gari da baiwa jama’a labarin sanarwar gwamnati na haramtawa dalibai mata amfani da Nikabi a cikin makarantun firamare da sakandare.

Sabuwar dokar ta kuma sanya amfani da hijabi ko kuma rufe kai a matsayin zabin da dalibai ke da shi ko dai su sa ko kuma su bar shi, ko kuma idan iyayen su sun tilasta musu.

To amma da alama wannan doka bata yiwa jama’ar kasar da ke da rinjayen mabiya addinin musulunci dadi ba, inda suka rika tofin ala tsine ga gwamnati musamman a shafukan su na X wato Twitter a baya.

To amma gwamnatin kasar ta dage kan cewa wannan wata hanya ce ta rage tsatsauran ra’ayin addinin Islama, abinda ya baiwa masu goyon bayan dokar ayyana duk mai yaki da ita a matsayin magoyin bayan kungiyar Taliban da kuma IS.

Duk da wannan ce-ce-kuce da ake yi har yanzu gwamnatin kasar bata ce komai game da dokar ba, abinda ke nufin ta tsaya kan matsayar ta na haramtawa ‘yan matan amfani da nikabi da kuma basu zabin rufe gashin su ko akasin haka.

Wannan mataki dai na zuwa ne makonni biyu bayan da kotun Faransa ta tabbatar da dokar hana amfani da hijabi ko kuma duk wani na’u’i na suturta jiki da mata musulmi ke yi a cikin makaratu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.