Isa ga babban shafi

Masar zata kafa dokar takaita haihuwa a kasar

Shugaban Masar, Abdel Fattah Al Sissi, ya ce za a dauki matakan da za su taimaka wajen rage yawan haihuwar da iyalai ke yi a sassan kasar, a fayyace dai kasar za ta yi koyi da irin matakan da kasar china ta dauka na rage yawan haihuwa.

Shugaban kasar yace lokaci yayi da ya kamata gwamnati ta shiga cikin lamarin haihuwa tsakanin ma'aurata
Shugaban kasar yace lokaci yayi da ya kamata gwamnati ta shiga cikin lamarin haihuwa tsakanin ma'aurata REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters.
Talla

Shugaban na Masar ya ce suna bukatar haihuwar akalla yara dubu 400 a shekara, yayin da kasar da ke da yawan al’umma miliyan 105 ta fitar da rahoton cewa yara miliyan biyu da dubu 200 aka haifa a shekarar 2022 kadai.

Al Sissi na wannan jawabin ne, bayan da ministan lafiya da kula da yawan jama’a na kasar Khaled Abdul Ghaffar, ya shaidawa wani taron manema labarai cewa haihuwar ‘yaya dai-dai yake da samun cikkaken ‘yanci.

Sai dai shugaban na Masar ya ce bai amince da wannan furuci ba, yana mai cewa idan har aka baiwa al'umma damar haihuwa barkatai to kuwa gwamnati ce za ta ji a jikinta.

Kasar China ce dai ta fara samar da dokar takaita haihuwa zuwa yaro daya tilo ga ma’aurata a duniya a shekarar 1968, sai dai a shekarar 2015 ne gwamnatin Beijing ta sassauta, inda aka bawa ma’aurata damar haihuwar yara biyu.

Al Sissi ya buga misali da kasar ta China, yana mai cewa ta wannan tsarin ne ta shawo kan matsalar haihuwa barkatai, kuma ta yi hakan ne domin kaucewa tabarbarewar lamura yayin da tattalin arzikinta ya shiga wani hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.