Isa ga babban shafi

An kashe ministan kwadagon Uganda

An harbe karamin Ministan Kwadago, na Uganda, Kanal Charles Okello Engola, mai ritaya da safiyar Talata a gidansa da ke unguwar Kampala.

Charles Okello Engola
Charles Okello Engola © Parliament of the Republic of Uganda
Talla

Shi ma mai taimaka wa ministan, Ronald Otim ya samu munanan raunuka kuma tuni aka garzaya da shi asibitin Mulago domin samun kulawar gaggawa.

Rahotanni sun ce, guda daga cikin dogaran karamin ministan ne ya harbe Engola a gidansa da ke Kyanja wanda ake zargin ya yi harbe harbe da dama kafin ya sheke shi.

Sai dai dogarin ya tsere daga wurin zuwa cibiyar kasuwanci da ke Kyanja, inda ya shiga wani shagon gyaran gashi kuma ya harbe kansa har lahira, kamar yadda kakakin ‘yan sanda, Fred Enanga ya shaida wa manema labarai a Kampala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.