Isa ga babban shafi

Museveni ya ki rattaba hannu kan dokar hukuncin ga masu auren jinsi daya

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ki sanya hannu kan sabuwar dokar da ta tanadi yanke hukuncin kisa ga mutanen da aka samu da aikata lafin zama masu dabi’ar aure jinsi daya, inda ya bukaci da yi mata kwaskwarima.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni.
Shugaban Uganda Yoweri Museveni. AP - Bebeto Matthews
Talla

Museveni ya sanar da matakin ne da yammacin ranar Alhamis bayan ganawa da ‘yan majalisa, wadanda kusan dukkaninsu ke goyon bayan kudirin dokar da suka amince da shi a watan jiya.

A wata sanarwa da ya fitar, kakakin shugaban ya ce Museveni baya adawa da hukuncin kisan, amma yana son 'yan majalisar su duba batun bayar da damar gyara halayyar masu dabi’ar ta auren jinsi daya idan da yiwuwar hakan.

Kasar Uganda na kan gaba tsakanin kasashen Afirka da suka alwashin sa kafar wando guda da duk wanda yake goyon bayan masu dabi’ar auren jinsi guda, duk sukar da gwamnatin Yoweri Museveni ke sha daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma manyan kasashen Turai da Amurka, wadanda a baya suka kakabawa shugaban na Uganda takunkumai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.