Isa ga babban shafi

Kenya, Tanzania, Uganda na son karbar bakuncin gasar AFCON ta 2027

Kasashen Kenya da Tanzaniya da Uganda sun kaddamar da wani shiri na hadin gwiwa kan neman karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2027.

Wasan da Gambia da Mali suka fafata a gassar ta AFCON a Limbe, na kasar Kamaru. yayin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta da aka yi a 2021/
Wasan da Gambia da Mali suka fafata a gassar ta AFCON a Limbe, na kasar Kamaru. yayin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta da aka yi a 2021/ © RFI/Sally Jeng
Talla

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika CAF ta ce ta samu tayin karbar bakuncin gasar daga kasashen uku tare da tayin Aljeriya da Botswana da Masar.

A cikin watan Disamba ne gwamnatin Kenya ta amince da kudirin majalisar ministocin kasar na mara baya ga yunkurin shiga gasar, tare da wasu makwabtanta guda biyu cikin msu neman karbar bakuncin gasar.

Gwamnatin ta ce, hakan zai taimaka wa kungiyar kwallon kafa ta Harambee Stars, wajen cimma burinsu na samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya a karon farko a shekarar 2030.

Ministan wasanni na kasar Kenya Ababu Namwamba ya ce ya tattauna da takwarorinsa na Uganda da Tanzaniya, inda ya kara da cewa suna shirin kafa kwamitin hadin gwiwa ka shirin karbar gaar.

Rashin wadatattun ababen more rayuwa na filin wasa ya kasance matsala ga galibin kasashen gabashin Afirka, abin da ya tilastawa kungiyoyin kasa buga wasannin nahiya a waje.

A watan Satumba ne CAF za ta bayyana sunan kasar da zata karbi bakuncin, da kuma inda za a gudanar da gasar shekarar 2025, bayan da aka hana wa Guinea mai masaukin baki ‘yancin karbar bakuncin gasar a watan Oktoban da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.