Isa ga babban shafi

Za mu aike da dakaru na musamman don bai wa Rasha kariya- Dan shugaban Uganda

Dan shugaba Yoweri Museveni na Uganda, Muhoozi Kainerugaba ya ce a shirye ya ke ya tura dakaru na musamman don bai wa Rasha kariya idan bukatar hakan ta taso.

Dan shugaban kasar Uganda Muhoozi Kainerugaba, da ke shirin tsayawa takarar zaben kasar.
Dan shugaban kasar Uganda Muhoozi Kainerugaba, da ke shirin tsayawa takarar zaben kasar. AP - Hajarah Nalwadda
Talla

Cikin sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Kainerugaba wanda Janar din Soja ne, ya ce idan an so za a iya kiranshi da babban masoyin Putin amma ko shakka babu Uganda a shirye ta ke ta bayar da kariya ga Rasha idan har akwai bukatar hakan.

Janar Kainerugaba da ya yi kaurin suna wajen tsoma baki a harkokin siyasar makwabta tare da yi musu barazanar Soji, ya ce kasashen yammaci na bata lokacinsu a farfagandar yakin Ukraine.

Dan shugaban kasar mai shekaru 48 wanda ya jima yana nuna goyon baya ga shugaba Vladimir Putin kalaman nasa na zuwa ne kwana guda bayan sanar da aniyarsa ta kafa tashoshin rediyo da talabijin masu sunanshi.

A watan jiya ne Kainerugaba ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a zaben Uganda na shekarar 2026, batun da aka jima ana jita-jitarsa.

Ko a watan Oktoban bara sai da shugaba Museveni ya haramtawa Janar Kainerugaba katsalandan a harkokin cikin gidan kasar da kuma yiwa makota barazana. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.