Isa ga babban shafi

An samu karancin rigakafin cutuka ga kananan yara a Nijar

Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke bayyana damuwa akan yadda kananan yara da dama a duniya basu samu damar karbar allurar rigakafi ba tunda daga shekarar 2020 saboda annobar korona, ma’aikatar lafiya Nijar ta tabbatar samun wannan matsala a cikin kasar ta. 

Samfurin rigakafin cutar shan inna kenan.
Samfurin rigakafin cutar shan inna kenan. Getty Images/iStockphoto - Hailshadow
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin yara miliyan 67 ne suka gaza samun allurar rigakafin a sassan duniya tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021, saboda kulle da aka tsaurara bayan bullar annobar Covid-19  da ta haifar da koma baya ga sha’anin kiwon lafiya ga kasashe, musamman matalauta.

Allurar riga kafi na ceto rayukan yara miliyan 4.4 a kowace shekara, adadin da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na iya haura miliyan 5.8 nan da shekarar 2030 idan an cimma burinta na barin babu kowa a baya.

SHiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Baro Arzika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.