Isa ga babban shafi
Masar-Morsi

An gudanar da Jana'izar Morsi cikin sirri a Masar

An gudanar da jana’izar tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi a Birnin Alkahira a asirce, da kuma masa addu’oi a Turkiya, yayin da Majalisar Dinkin Dinkin Duniya ta bukaci gudanar da bincike mai zaman kan sa kan mutuwar.

Sallar Jana'izar tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi
Sallar Jana'izar tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi REUTERS/Murad Sezer
Talla

Rahotanni daga birnin Alkahira sun ce an birne tsohon shugaban kasa Mohammed Morsi ne a wata makabartar da ke Medinat Nasr, a Gabashin Birnin Alkahira cikin matakan tsaro, yayin da lauyan sa Abdel Moneim Abdel Maksoud ya bayyana cewar iyalan sa suka wanke shi, suka masa Sallah a asibitin Lemman Tora kafin birne shi.

Lauyan yace shi da akalla mutane 10 daga cikin iyalan sa da kuma abokan huldar sa suka halarci jana’izar.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa yace an hana Yan Jaridu shiga makabartar inda aka birne daruruwan mutanen da aka yiwa kisan gilla a watan Agustan shekarar 2013, cikin su harda mutane 800 da aka kashe a rana guda.

A kasar Turkiya kuwa, dubban mutane ne suka halarci jana’izar tsohon shugaban na Masar kamar yadda hukumar kula da addinin kasar at kira, yayin da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya cacaki kasashen duniya kan yadad suka zuba ido suna kallon yadad aka yiwa Morsi juyin mulki kana aka tsare shi a daki guda.

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Amnesty International da Human Rights Watch da Dan Majalisar Birtaniya sun bukaci gudanar da bincike kan mutuwar tsohon shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.