Isa ga babban shafi
Masar

Sojin Masar sun hallaka 'yan ta'adda 38 tare da kame 500

Rundunar sojin Masar ta sanar da samun nasarar hallaka akalla mayakan kungiyoyin ta’addanci 38 baya ga kame wasu fiye da 500. Sanarwar Rundunar sojin na zuwa ne kwanaki kadan bayan kaddamar da sabon farmaki kan kungiyoyin mayakan da suka yi wa kungiyar IS mubaya’a yankin Sinai.

Masar ta shafe shekaru ta na yaki da mayakan sa kai da ke yi wa gwamnatin bore, musamman a yankin Sinai da hare-hare kan jami’an tsaron kasar ke dada karuwa a baya bayan nan.
Masar ta shafe shekaru ta na yaki da mayakan sa kai da ke yi wa gwamnatin bore, musamman a yankin Sinai da hare-hare kan jami’an tsaron kasar ke dada karuwa a baya bayan nan. AFP
Talla

Sanarwar ta ci gaba da cewa daga cikin mayakan kungiyoyin ta’addancin 38 da suka hallaka har da guda 10 da suka shirya wasu muggan hare-hare da suka hallaka daruruwan Mutane a yankin na Sinai.

Shugaba Abdul Fatah alsisi dai ya sha alwashin kawar da ayyukan ta'addanci a kasar ta Masar, yayin da a lokuta da dama ke umartar jami'an tsaro da kai mabanbantan farmaki kan maboyar 'yan ta'addan.

Kakakin sojin na Masar Kanal Tamer Rifai ya ce ko a makon jiya sun kaddamar da makamantan hare-haren a yankunan kasar da su ke yamma da Hamada, domin murkushe kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Tuni dai rundunar sojin Masar ta kara matakan tsaro a asibitocin da ke kasar da kuma shirya daukar matakan bada agajin gaggawa da samar da magunguna. Zalika rundunar sojin ta kara matakan tsaro a ilahirin tashoshin jiragen ruwa na kasar.

Masar ta shafe shekaru ta na yaki da mayakan sa kai da ke yi wa gwamnatin bore, musamman a yankin Sinai da hare-hare kan jami’an tsaron kasar ke dada karuwa a baya bayan nan.

Akalla mutane 235 suka hallaka a wani harin bam da aka kai kan wani Masallaci a arewacin yankin Sinai, a lokacin da mutanen suke tsaka da gabatar da Sallah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.