Sojin Masar sun kaddamar da sabon farmaki kan 'yan ta'adda
Rundunar sojin Masar ta kaddamar da farmaki a sassann kasar, kan kungiyoyin ‘yan ta’adda da kuma sauran gungun masu aikata laifuka.
Wallafawa ranar:
Kakakin sojin na Masar Kanal Tamer Rifai ya ce sun kaddamar da farmakin ne a Yankin Sinai, da kuma yankunan kasar da suke yamma da Hamada, domin murkushe kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Tuni dai rundunar sojin Masar ta kara matakan tsaro a asibitocin da ke kasar da kuma shirya daukar matakan bada agajin gaggawa da samar da magunguna. Zalika rundunar sojin ta kara matakan tsaro a ilahirin tashoshin jiragen ruwa na kasar.
Masar ta shafe shekaru tana yaki da mayakan sa kai da ke yi wa gwamnatin bore, musamman a yankin Sinai da hare-hare kan jami’an tsaron kasar ke dada karuwa a baya bayan nan.
Akalla mutane 235 suka hallaka a wani harin bam da aka kai kan wani Masallaci a arewacin yankin Sinai, a lokacin da mutanen suke tsaka da gabatar da Sallah.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu