Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta sake karbe Marte

Rahotanni daga Najeriya na cewa Mayakan Boko Haram sun sake karbe ikon garin Marte bayan sun kori sojojin kasar daga yankin. Wasu majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa mayakan na Boko Haram sama da 2,000 sun yi musayar wuta da dakarun Najeriya tun daga garin Kerenowa har zuwa Marte.

Sojojin Najeriya da Kamaru da ke yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya da Kamaru da ke yaki da Boko Haram AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Majiyoyin sun ce ‘Yan Boko Haram sun kashe mutane da dama.

Wannan ne dai karo na uku da mayakan Boko Haram ke karbe ikon Marte da ke kan iyaka da tabkin Chadi a cikin Jihar Borno.

Sai dai kuma duk da cewa wata majiyar sojin Najeriya ta tabbatar da labarin harin na Marte amma majiyar ba ta tabbatar da ko mayakan Boko Haram sun karbe ikon garin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.