Mayakan Huthi na neman zaman barazana ga sauran kasashen Duniya
Mayakan Huthis a Yamen na ci gaba da kokarin karbe ikon wuraren bincike dake garin Bab Al-Mandab da ke kudancin kasar, yanzu dai hankula al’ummar kasar a tashe yake, ganin yadda yunkurin mayakan ke barazana ga tsaron kasar dama na sauran kasashen Duniya
Wallafawa ranar:
A jiya lahadi mayakan suka karbe ikon filin jirgin sama dake birnin Taez abinda ke kara barazana ga tsaron Shugaban kasar Abdelrabuh Mansour Hadi da yanzu haka ke samun mafaka a birnin Aden
Shugaba Hadi ya tsere ne daga daurin talala, a makon da ya gabata, kasar Yemen ta fada cikin rikici, sakamakon rarabuwar kawuna tsakanin mayakan Huthis da magoya bayan Shugaban kasar
Yanzu dai masana sun ce idan har mayakan Huthis sun yi nasarar karbe ikon wuraren binciken kan ruwa to hakika kasar zata fada cikin rikicin da zai zama matsala ga sauran kasashen duniya
Masanan sun bayyana dangatakar da mayakan na Huthis ke da Iran wanda acewar su nasarar ga mayakan Huthis nasara ce da kasar Iran zata yi marhabun da ita ganin haka zai taimaka mata a shirin Nukiliyar kasar
Tuni dai kwamitin Sulhu na MDD ya bayyana amincewar sa ga Gwamnatin Shugaban kasar Mansour Hadi da Gwamnatin hadin kan kasar da yanzu haka mayakan houthi ke neman kawar wa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu