Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 35 suka mutu a hare haren Jos da Biu

Akalla mutane 35 aka tabbatar da mutuwarsu a hare haren bama bamai da aka kai a garuruwan Jos na Jihar Filato da Biu na Jihar Borno a Najeriya. Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba Goodluck Jonathan ya kai ziyara garin Baga bayan Sojin kasar sun kwato garin daga hannun Mayakan Boko Haram inda suka kashe mutane da dama.

Mutane da dama suka jikkata a hare haren da aka kai a biranen Kano da Potiskum da Biu da Jos a arewacin Najeriya
Mutane da dama suka jikkata a hare haren da aka kai a biranen Kano da Potiskum da Biu da Jos a arewacin Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Mutane 18 suka mutu a harin Biu bayan da wani dan kunar bakin wake ya dala wa kansa bom a Tashar Motar da ake kira Tashar Gandu.

Wani mazaunin garin Biu ya shaidawa RFI Hausa cewa ‘yan kunar bakin wake Mace da Namiji ne suka kai harin, amma akwai wani dan kunar bakin waken da aka harbe har lahira kafin ya tarwatsa kansa.

A garin Jos na Jihar Flato ma mutane 17 aka tabbatar da mutuwarsu a hare haren kunar bakin wake guda biyu da aka kai a wata tashar Mota da ke tsakiyar garin.

Wadannan hare haren na zuwa ne bayan hare haren da aka kai a biranen Kano da Potiskum inda mutane 51 suka mutu.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai wanna harin. Sai dai ana zargin kungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a yankin arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.