Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Kotun ICC ta ce dole a gurfanar da matar Laurent Gbagbo a gabanta

Kotun hukunta masu laifukan yaki ta Duniya wato ICC ta ki amincewa da bukatar sauraron karar da aka shigar akan Matar tsohon shugaban kasar Cote D’ivoire wato Simone GBagbo a gida, maimakon gurfanar da ita a gaban Kotun

ladepechedabidjan.info
Talla

A wata sanarwar da ta fitar a birnin Hague Kotun ta bayyana yin fatali da bukatar barin matar tsohon shugaban kasar ga Hannun hukumomin kasar ta Cote d'Ivoire.

Baya ga kin amincewa da bukatar gwamnatin kasar Cote D’Ivoire, Kotun ta ICC haka ma ta gargadin hukumomin kasar da su tabbatar sun sallama mata wadda ake tuhuma wato matar tsohon shugaban kasar Simone Gbagbo, domin a gurfanar da ita a gaban Kuliya manta sabo.

Idan ana iya tunawa dai a shekaru 2 da suka gabata ne Kotun ta ICC, ta gabatar da Sammacin kama Simone Gbagbo mai shekaru 65, bisa zargin da ake mata da Hannu ga tashin hankalin shekarar 2010 da ya yi sanadin mutuwar mutane 3,000, zargin da ake mata da Mijinta baki daya.

Musabbabin tashin hankalin dai shi ne kememen da mijinta Larent GBagbo ya yi a wannan shekarar, bayan da ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar.

 

Bayan kammala fadan ne dai aka kama Simone Gbagbo da mijinta Laurent Gbagbo, amma aka mika shi mijin nata Gbagbo ga Kotun ta ICC bayan akalla Watanni 7 da gudanar da rikici.

Tun a wannan lokacin ne dai Simone Gbagbo ke zaman Kaso a cikin kasar, yayin da hukumomin kasar ke ta jan Kafa kan batun mikata ga Kotu.

A watan Yulin shekara mai kamawa ne dai ake sa ran yankewa mijinta Laurent Gbagbo hukuncin da ya dace da shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.