Isa ga babban shafi
Libya

An tsagaita wuta a Benghazi

Majalisar Dinkin Duniya tace mayakan sa-kai da ke rikici a kasar Libya sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon sa’o’I 12 a Benghazi domin samun damar shigar da kayan jin kai a cikin kasar.

Mayakan sa-kai a  Benghazi
Mayakan sa-kai a Benghazi REUTERS/Stringer
Talla

Wannan ne karon farko da bangarorin biyu suka amince su tsagaita wuta. Amma wakilin Kamfanin Dillacin labaran Faransa yace ya ji karar harbin bindiga bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce matakin tsagaita wutar zai bayar da damar a fice da fararen hula tare da shigar kayan agaji.

Mutane sama da 350 ne aka kashe tun lokacin da Mayakan sa-ai da ke samun goyon bayan gwamnati suka kaddamar da yaki akan Mayakan da ke da’awar Shari’a da suka kwace ikon garin Benghazi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.