Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta nemi a binciki yarjejeniyar tsagaita wuta

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Jam’iyyar APC mai adawa a Najeriya ta bukaci a gudanar da bincike akan batun yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin ta cim ma da Mayakan Boko Haram.

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP
Talla

Jam’iyyar APC mai adawa ta yi kira a kafa kwamiti na musamman domin nazarin yarjejeniyar tsagaita wutar bayan Shugaban Boko haram ya fito ya yi karyata ikirarin.

Sanarwar da kakakin Jam’iyyar Lai Muhammaed ya sanya wa hannu, APC ta yi kira ga gwamnatin Goodluck Jonathan ta fito ta fadawa ‘Yan Najeriya gaskiyar abin da ke faruwa, maimakon yin wasa da hankalin ‘yan kasar.

Shugaban Boko haram dai ya fito a cikin wani sakon bidiyo yana karyata batun tsagaita wuta da gwamnati, tare da cewa ya aurar da ‘Yan Matan Chibok.

Jam’iyyar ta APC tace yanzu babu wanda ya san makomar ‘Yan Matan Chibok sama da 200 da mayakan Boko Haram suka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.