Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya suna nazarin bidiyon Shekau

Rundunar Sojin Najeriya tace tana nazarin sabon sakon bidiyon shugaban Mayakan Boko Haram Abubakar shekau, game da batun ‘Yan matan Chibok da kuma yarjejeniyar tsagaita wuta da ya karyata sun cim ma tsakanin shi da gwamnati.

Chris Olukolade, Kakakin rundunar sojin Najeriya
Chris Olukolade, Kakakin rundunar sojin Najeriya AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Sojin kasar Chris Olukolade, ya sanya wa hannu, Sojin na Najeriya sun ce zasu sanar da matsayinsu ga ‘Yan Najeriya game da sabon sakon bidiyon idan sun kammala nazari akansa.

A cikin bidoyon Shekau ya yi watsi da ikirarin sun sasanta da gwamnatin Najeriya, tare da cewa ya aurar da ‘Yan matan Chibok bayan ya musuluntar da su.

Amma cikin sanarwar Mr Olukolade ya jaddada cewa zasu ci gaba da bin matakan sulhu domin kubutar da ‘Yan matan na chibok su sama da 200 da ke hannun Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.