Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kafa sabuwar daula a Najeriya

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin kafa daular musulunci a arewacin Najeriya a cikin wani sakon bidiyo da aka aikawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa, bayan Mayakansa sun kwace Gwoza da ke cikin Jihar Borno.

Aboubakar Shekau Shugaban Mayakan Boko Haram a Najeriya
Aboubakar Shekau Shugaban Mayakan Boko Haram a Najeriya AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

A cikin bidiyon na tsawon Mintina 52, Shekau ya ayyana kansa a matsayin Kalifan sabuwar daular da ya kafa.

Shekau ya yi ikirarin cewa Najeriya ba ta da iko da Gwoza, domin ta dawo karkashin ikon shi.

A cikin Jawabinsa, Shugaban na Boko Haram yace za su dawwama a Gwoza, domin ba zasu fice ba.

Daruruwan Mutanen Gwoza ne dai suka tsere daga garin bayan Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hare hare inda suka kwace wata kwalejin horas da ‘Yan sanda.

Rahotanni sun ce Mayakan na Boko Haram sun kwace garin Buni Yadi a Jihar Yobe kuma suna cin karensu ba babbaka a kudancin Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.