Isa ga babban shafi
Najeriya

Olukolade: Ana zuga Sojoji su yi bore

Rundunar Sojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke cewa wasu dakarun kasar sun yi bore a jihar Borno, a lokacin da aka tura su domin tunkarar Mayakan kungiyar Boko Haram a Gwoza. Janar Chris Olukolade mai magana da yawun rundunar, yace Sojojin kasar masu kishin kasa ne.

Kakakin rundunar Sojin Najeriya, Chris Olukolade.
Kakakin rundunar Sojin Najeriya, Chris Olukolade. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

“Sojojin Najeriya suna da da’a, masu saudaukar da kai da kwazo ba matsorata ba ne ” a cewar Olukolade.

Mr Olukolade yace wanda ya kawo wannan labarin yana neman ya zuga sojoji kasar ne don su yi bore, yana mai cewa sojojin Najeriya ba zasu yarda da zuga ba.

Sojoji da dama ne suka yi bore saboda rashin nagartattun makamai da zasu tunkari Mayakan Boko Haram a Jihar Borno, kamar yadda wasunsu suka tabbatarwa RFI Hausa.

Amma Janar Olukolade ya karyata zargin akan Sojoji suna fatarar Makamai, yana mai cewa wannan wani yunkuri ne karya ma su kwarin gwiwa.

“Ba sojan da aka tura fagen fama ba tare da an ba shi makamai ba”.

Mr Lokolade yace wannan zargi na ruruta rikici da matsalar tsaro a Najeriya.

Ikirarin Olukolade dai ya yi karo da bukatar da Shugaban Najeriya ya shigar a gaban Majalisa akan su amince ya ciwo bakin kudi domin samar da kayan aiki ga Sojoji.

A kwanakin baya, Gwamnan Jihar Borno Kashin Shettima ya taba fada cewa Mayakan Boko Haram sun mallaki manyan makamai fiye da Dakarun Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.