Isa ga babban shafi
Najeriya

Bam ya tashi a unguwar Sabon Gari da ke Kano

Rahotanni daga Najeriya sun ce bam ya fashe a cikin wata tashar mota da ke birnin Kano na arewacin kasar a marecen yau alhamis.

Wani Mutum kusa da inda aka kai harin Bom a tashar Motoci da ke sabon Garin Kano wanda ya ti sanadiyar hasarar rayuka 25 bayan tashin jerin bama bamai 5
Wani Mutum kusa da inda aka kai harin Bom a tashar Motoci da ke sabon Garin Kano wanda ya ti sanadiyar hasarar rayuka 25 bayan tashin jerin bama bamai 5 REUTERS/Stringer
Talla

Shaidun gani da ido sun ce bam din wanda bisa ga dukkan alamu an ajiye shi ne a cikin wata jaka, ya fashe ne a cikin wata tasha da ke unguwar Sabon Gari, kuma shaidu sun tabbatar da cewa fashewar ta haddasa barna mai tarin yawa.

Kawo yanzu dai babu cikakkun bayanai a game da wannan hari, da ya faru kwana daya bayan hare-haren bam da aka kai a garin Kaduna da arewacin kasar, wadanda suka sanadiyyar mutuwar mutane masu tarin yawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.