Isa ga babban shafi
Mali

Kungiyar al-Qaeda ta dau alhakin kashe 'yan jaridan Faransa

Kungiyar Alqaeda reshen Arewaci da Yammacin nahiyar Africa ta fitar da wata sanarwa dake ikirarin itace ta hallaka ‘yan jaridun nan biyu na kasar Faransa a kasar Mali.Su dai wadannan ‘yan jaridu biyu na gidan Radion Faransa Gislain Dipon mai shekaru 57 da kuma Klod Verlon mai shekaru55 , sace su akayi bayan sun kammala tattaunawa da wani mai Magana da yawun ‘yan tawaye a yankin Kidal dake kasar ta Mali.Sanarwar da kungiyar ta bayar na cewa kisan wadannan ‘yan jaridu, martani ne zuwa ga kasar Faransa saboda abubuwan da tayi a kasar ta Malj.Acewar sanarwar wadda aka yada ta kafofin yada labarai dake yankin Sahara wannan biyan wani karamin bashi ne da kasar Faransa ta ciyo.Kungiyar tace wani kwamandan kungiyar mai suna Abdulkarim Targui, na kusa da Abdelhamid Abou Zeid, daya daga cikin manyan dakarun kungiyar Alqaeda a Mali wanda aka kashe a lokacin da suke fafatawa da sojan kasar Faransa.‘Yan awoyi kadan ne dai sojan Faransa dake sintiri suka tsinci gawan mamatan biyu a daji. 

Gislain Dipon da Klod Verlon, da aka kashe a Mali
Gislain Dipon da Klod Verlon, da aka kashe a Mali
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.