Isa ga babban shafi
Guinea-Bissau

Shugaban Guinea Bissau Malam Bacai Sanha ya mutu a asibitin kasar Faransa

Shugaban kasar Guinea-Bissau Malam Bacai Sanha ya mutu a wani asibiti dake birnin Paris na kasar Faransa yau Litinin, kamar yadda sanarwar gwamnatin kasar ta Guinea Bissau ta tabbatar.

Shugaban kasar Guniea Bissau Marigayi Malam Bacai Sanha
Shugaban kasar Guniea Bissau Marigayi Malam Bacai Sanha AFP / Pius Utomi Ekpei
Talla

Dan shekaru 64 tun kafin bukin Kirsimati aka kwantar dashi a Asibitin Soja mai suna Val De Grace dake birnin na Paris.

Tun da ya fara ciwon anki bari kowa ya san irin cutar da yake fama da ita. Zuwa wani lokaci za a bayyana yadda za ayi zana'idar.

Yanzu haka shugaban majalisar dokokin kasar ta Guinea Bissau Raimundo Pereira, daga jam'iyya mai mulki ta Marigayi Sanha, zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamnatin rikon kwarya kafin zabe.

Bisa tsarin mulkin kasar cikin kwanaki 90 za a gudanar da zabe.

Cikin shekara ta 2009 Bacai Sanha ya lashe zaben da aka gudanar, bayan kisan gillar da aka yi washugaban kasar na wannan lokaci Joao Bernardo Vieira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.