Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

An Tsare Tsohon babban Habsan Sojan Guinea

Tsohon shugaban rundunar sojan kasar Guinee Conakri Genar Nouhou Thiam ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, tun ranar larabar da ta gabata a ke tsare da shi a ma’aikatar jandarmu dake birnin Conakri, ba tare da sannin takamaiman laifin da ya aikata ba, inda ya zargin sojoji da kokari shafa masa kashin kaji.Janar Thiam ya bayyana cewa, bai san dalilin aje shi a inda yake ba, kuma babu wanda ya zo ya yi masa karin haske dangane da dalilin rike shi, inda ya kara da cewa, akwai sojojin da ba su yarda da demokradiya ba, wadanda kuma suke ganin, ya zama tamkar kadangaren bakin tulu, sai sun kauda shi ne, kafin su cimma bukatunsu in ji shi.

Sojojin Guinea Conakry
Sojojin Guinea Conakry Reuters / Joe Penney
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.