Isa ga babban shafi
Syria

Rasha da China sun nuna damuwarsu kan harin da Isra’ila ta kai Syria

Kasashen Rasha da China sun bayyana damuwar su kan abinda zai biyo baya a Yankin Gabas ta tsakiya, sakamakon harin da Isra’ila ta kai Syria. Rasha ta ce tana fargabar cewar an dada matsawa lokacin yin amfani da sojojin kasashen waje a Syria, musamman kan zargin amfani da makami mai guba. 

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Alexei Nikolsky/Ria Novosti/Pool(
Talla

Wannan damuwa da kasashen biyu suna nuna, na zuwa ne a dai dai lokacin da Dubban mutane ne suka gudanar da zanga zanga a birnin Moscow, dan nuna adawa da shugabancin Vladimir Putin, wanda ya karbi ragamar tafi da kasar bara.

Wadanda suka shirya zanga zangar sun ce, dubun dubantan mutane ne suka shiga zanga zangar, sai dai ‘Yan Sanda sun ce mutane 8,000 kawai.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.